Fim ɗin wata shida ya samu yabo a wajen masu kallo da manyan masu harkar Fim ɗin Hausa

0
9

Fim ɗin wata shida ya samu yabo a wajen masu kallo da manyan masu harkar Fim ɗin Hausa

Fim ɗin wata shida, mai dogon zango ya samu yabo a wajen al’ummar dake kallon fina-finan Hausa da kuma su kansu masana harkokin shirya fim da bayar da umurni.

Tabbacin hakan ya samu a yayin da aka gudanar da taron nuna gamsuwa da fim da wanda ya gudana a birnin Kano, a daren Lahadi, ta hanyar yin liyafa da zantawa da jaruman fim ɗin da masu kallo har ma da manyan jaruman Kannywood.

Shugaban hukumar dake kula da harkokin fina-finai ta kasa kuma daya daga cikin jaruman fim ɗin wata shida Ali Nuhu Muhammad, ya bayyana cewar tabbas anyi amfani da hikima tare da ƙwarewa a wajen shiryawa da bayar da umurnin fim ɗin wanda hakan ne yasa aka samu nasara a aikin fim ɗin.

Shima a shugaban hukumar tace fina-finai da ɗab’i ta jihar Kano, Abba Almustafha, cewa ya yi bai yi mamakin ganin nasarar da fim ɗin wata shida ya samu ba, sakamakon an haɗa mutanen da suka san aiki da jajircewa wajen shirya fim ɗin.

Hayatuddeen Yakubu, shi ne mashiryin shirin, yayin da Ɗan Hausa, ya bayar da umarni.

Suma masu kallon wannan fim maza da mata ba’a bar su a baya ba domin sun halarci liyafar tare da bayyana gamsuwa da yadda aka gabatar da shirin.

Fim ɗin wata shida dai ya samu nasarar zama daya daga cikin fina-finan da mutane suka fi kallo a nahiyar Afirka.

Daga cikin fitattun jaruman Kannywood da suka halarci taron akwai, Shehu Hassan Kano, Ibrahim Madawari, Daddy Hikima, Fatima Hassan da kuma mawakan Hausa irin su Dafo da Prop.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here