Sojoji sun kama shahararren ɗan bindiga a jihar Benue

0
10

Dakarun Rundunar Sojin Najeriya da ke ƙarƙashin sansanin FOB Wukari a jihar Taraba, sun kama wani shahararren jagoran ’yan bindiga da ake nema ruwa a jallo a jihar Benue, mai suna Fidelis Gayama.

An kama Fidelis Gayama, a ranar 21 ga Disamba, 2025, a ƙauyen Vaase da ke ƙaramar hukumar Ukum ta jihar Benue, bayan wani samame na musamman da aka gudanar bisa sahihan bayanan sirri.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Laftanar Umar Muhammad, ya bayyana cewa Gayama yana cikin jerin manyan ’yan bindigar da hukumomin tsaro ke nema a jihohin Benue da Taraba.

Binciken farko ya nuna cewa wanda aka kama yana da alaƙa da shahararren jagoran ’yan bindiga Aka Dogo, kuma ana zargin sa da jagorantar wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane da fashi da makami da ke addabar matafiya da al’ummomi a hanyar Kente–Wukari da yankunan kan iyakar Benue da Taraba.

Rundunar sojin ta ce an riga an tsare wanda ake zargin, kuma za a miƙa shi ga hukumomin da suka dace domin zurfafa bincike da gurfanar da shi a gaban kotu, bisa tanadin doka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here