Amurka ta janye jakadan ta daga Najeriya

0
7
Screenshot

Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya bayar da umarnin janye Jakadan Amurka a Nijeriya, Richard Mills, a wani sabon sauyin diflomasiyya da ya shafi ƙasashe da dama a duniya.

Rahotanni sun nuna cewa sama da ƙasashe 20 ne abin ya shafa, inda nahiyar Afirka ta fi fuskantar sauyin.

 Nijeriya na cikin ƙasashe 15 na Afirka da aka janye jakadun su, tare da wasu ƙasashe kamar Masar, Senegal, Rwanda, Uganda, Nijar da Kamaru.

Haka kuma, an samu irin wannan sauyi a wasu ƙasashen Asiya da Turai, da kuma yankin Amurka ta Tsakiya da ta Kudu.

Jami’an ma’aikatar harkokin wajen Amurka sun bayyana cewa an sanar da jakadun tun makon da ya gabata cewa wa’adin aikin su zai ƙare a watan Janairu mai zuwa. 

Duk jakadun da aka janye an nada su ne a zamanin mulkin tsohon shugaban Amurka, Joe Biden.

An ce matakin ya sauya ne bayan da a farko an bar wasu daga cikin su, sai dai daga baya aka fara aika musu da saƙon komawa birnin Washington domin karɓar wasu ayyuka.

Richard Mills ya fara aiki a matsayin jakadan Amurka a Nijeriya ne a watan Mayun bara. 

Janyewarsa na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun ɗan tangardar dangantaka tsakanin Nijeriya da Amurka, musamman kan batutuwan biza da tsaro.

Duk da haka, ɓangarorin biyu na ci gaba da tattaunawa domin ƙarfafa haɗin gwiwa, musamman a fannin tsaro da yaƙi da ta’addanci a yankin yammacin Afirka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here