Gwamnatin ta bayar da hutun Kirsimeti da sabuwar shekara

0
7
Tinubu
Tinubu

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Laraba 25 ga Disamba da Alhamis 26 ga Disamba, 2025 a matsayin ranakun hutu domin bikin Kirsimeti da Boxing Day.

Haka kuma, gwamnatin ta ayyana Laraba 1 ga Janairu, 2026 a matsayin hutun Sabuwar Shekara.

Bayanin hakan na cikin wata sanarwa da babbar sakatariya ta Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Dakta Magdalene Ajani, ta fitar a ranar Litinin, a madadin Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo.

A cikin sanarwar, ministan ya buƙaci ‘yan Najeriya su yi tunani kan darussan ƙauna, zaman lafiya, tawali’u da sadaukarwa da ke tattare da haihuwar Annabi Isa (A.S).

Ya kuma yi kira ga ‘yan ƙasa, ba tare da la’akari da addini ko ƙabila ba, da su yi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’a domin zaman lafiya, inganta tsaro da cigaban ƙasa.

Ministan ya ƙara da jan hankalin jama’a da su kasance masu bin doka da oda, tare da kula da tsaro yayin bukukuwan, yana mai yi wa ‘yan Najeriya fatan Kirsimeti mai albarka da Sabuwar Shekara mai cike da alheri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here