Kwamitin sabuwar dokar haraji ya yi ƙarin haske kan amfani da asusun banki a sabuwar shekara 

0
9

Shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Manufofin Kuɗi da Gyaran Haraji, Taiwo Oyedele, ya kwantar wa da yan Najeriya hankali kan sabuwar dokar haraji da za ta fara aiki daga 1 ga Janairu, 2026, inda ya ce ba za a toshe asusun bankin kowa ba saboda rashin lambar biyan haraji wato TIN.

Oyedele ya bayyana hakana Lagos inda ya ce manufar gyaran harajin ba wai ƙara wa mutane nauyin haraji ba ce, illa dai gina amincewa tsakanin gwamnati da al’umma.

“Gyaran haraji ba kawai magana ce ta kuɗi ko ƙididdiga ba, magana ce ta adalci da amincewa. Mutane na son sanin dalilin biyan haraji da yadda ake amfani da kuɗinsu, inji shi.”

Batun TIN da Asusun Banki

Oyedele ya jaddada cewa:

Ba za a hana mutum amfani da asusun bankin sa ba saboda rashin TIN, inda yace amma mutum ba zai iya buɗe sabon asusun banki ba idan ba shi da TIN.

A cewar sa, gyaran harajin an tsara shi ne domin kare talakawa, tabbatar da adalci, da ƙarfafa tattalin arziki, tare da ƙara gaskiya da bin doka a tsarin harajin Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here