Cunkoson ababen hawa ya tsare matafiya a hanyar Lokoja zuwa Abuja 

0
7

Matafiya da direbobi da ke bin babbar hanyar Lokoja zuwa Abuja sun makale a cunkoson ababen hawa mai tsanani, kwanaki kaɗan kafin bikin Kirsimeti.

Rahotanni sun nuna cewa cunkoson ya shafe kwanaki uku ana fama da shi, inda motoci suka kasa motsi, musamman a yankin Koton Karfe na jihar Kogi.

Wasu direbobi sun shaida wa gidan talabijin na NTA cewa sun kwana a kan hanya ba tare da sanin lokacin da za a samu sauƙi ba. 

Wani direba ya ce tun ƙarfe 7 na safe yake kan hanya tare da iyalansa, amma zuwa 8 na dare har yanzu ba su motsa ba.

Bincike ya nuna cewa manyan motocin dakon kaya biyu da suka faɗi a hanya ne suka haddasa wannan cunkoso, lamarin da ya jawo taruwar motoci har na tsawon mil uku zuwa biyar.

Saboda haka, wasu fasinjoji sun tilasta wa kansu bin hanyoyin karkara masu ƙura domin kauce wa cunkoson.

Jami’an tsaro ciki har da na Hukumar Kiyaye Hadurra ta Ƙasa (FRSC) sun isa wajen domin taimakawa rage cunkoso da daidaita zirga-zirga.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here