Gwamnatin Amurka ta sanar da ƙulla wata sabuwar yarjejeniya da Nijeriya domin ƙarfafa fannin kiwon lafiya a ƙasar, makonni kaɗan bayan wasu kalamai da Shugaba Donald Trump ya yi kan batun tsaro da addini a Nijeriya.
A cewar Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, yarjejeniyar za ta ɗauki tsawon shekaru biyar, inda Washington za ta kashe kimanin dala biliyan 2.1 wajen yaƙi da cututtuka kamar HIV, tarin fuka, zazzaɓin cizon sauro da cutar polio, tare da inganta lafiyar mata masu juna biyu da yara.
Har ila yau, Nijeriya ta yi alƙawarin zuba dala biliyan 3 a cikin wannan lokaci domin tallafa wa shirye-shiryen kiwon lafiyar.
Bayanan Amurka sun nuna cewa yarjejeniyar ta haɗa da tallafawa wasu cibiyoyin kiwon lafiya da ke da alaƙa da majami’u, abin da ya janyo muhawara dangane da batun addini.
A baya-bayan nan, Trump ya yi ikirarin cewa ana kai wa Kiristoci hare-hare a Nijeriya, har ma ya yi barazanar cewa Amurka za ta iya ɗaukar mataki idan lamarin ya ci gaba.
Sai dai gwamnatin Nijeriya ta musanta wannan zargi, tana mai jaddada cewa ba ta yarda da tsangwamar addini, kuma doka tana bai wa kowane ɗan ƙasa ‘yancin addininsa.
Masana sun bayyana cewa matsalolin tsaro da Nijeriya ke fuskanta sun shafi dukkan addinai da kabilu, inda rikice-rikice suka yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da tilasta wa miliyoyi barin muhallansu.


