Wata mummunar gobara ta tashi cikin tsakar dare a kasuwar masu aikin katako da ke unguwar Tal’udu a birnin Kano, lamarin da ya jefa ’yan kasuwa cikin tashin hankali tare da salwantar da dukiya mai yawa.
Wasu shaidun gani da ido sun bayyana cewa gobarar ta fara ci da misalin ƙarfe 2:30 na dare, inda wutar ta bazu cikin sauri sakamakon kayan katako da ke yankin.
Rahotanni sun nuna cewa wutar ta shafi shaguna da dama da ke kusa da gidan man fetur na WAA Rano, kuma ta ci gaba da ci na tsawon awanni kafin a samu nasarar kashe ta.
Zuwa yanzu dai, hukumomi ko waɗanda abin ya shafa ba su fitar da cikakken bayani kan adadin asarar da aka yi ba.


