Mutane 12 Sun Rasa Rayukansu a Mummunan Hatsarin Mota a Kogi

0
10

Aƙalla mutane 12, ciki har da yaro ɗaya, sun rasa rayukan su yayin da wasu biyu suka jikkata sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya faru a jihar Kogi.

Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa, FRSC, ta tabbatar da faruwar hatsarin wanda ya auku a daren Juma’a da misalin ƙarfe 11:30, a kan babbar hanyar Ejule zuwa Enugu, a yankin Iboko da ke ƙaramar hukumar Idah.

Kwamandan FRSC na jihar Kogi, Tenimu Etuku, ya bayyana cewa hatsarin ya shafi motar bas mai kujeru 18 (Toyota Hiace) mallakin kamfanin Romchi Mass Transit da wata babbar mota.

A cewar sa, motar ta yi karo da babbar mota da ta lalace wadda aka bari a kan hanya, lamarin da ya faru sakamakon yin gudu fiye da kima.

Etuku ya ce jami’an FRSC sun kai ɗauki cikin gaggawa, inda aka garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Mercy of Jesus da ke Ejule, yayin da aka ajiye gawarwakin mamatan a ɗakin ajiye gawa.

Ya bayyana hatsarin a matsayin abin tausayi da takaici, tare da miƙa ta’aziyyar sa ga iyalan waɗanda suka rasu. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here