Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar wa da majalisun dokokin ƙasa kasafin kuɗin shekarar 2026, wanda ya kai Naira triliyan 58.47.
A cewar shugaban ƙasar, an ware Naira triliyan 26.08 don ayyukan raya ƙasa, yayin da ayyukan yau da kullum zasu laƙume Naira triliyan 15.25.
Kasafin ya dogara da farashin gangar mai dala akan Dala 64.85.
Jimillar kuɗaɗen shigar da ake sa ran samu a 2026 sun kai Naira triliyan 34.33.
Kasafin ya kuma dogara da samar da gangar mai miliyan 1.84 a rana, da kuma farashin musayar kuɗi ₦1,400/$1.
Fannin tsaro zai laƙume Naira triliyan 5.41.
Manyan Ayyukan Gine-gine: Naira 3.56 tiriliyan
Ilimi: Naira triliyan 3.52 tiriliyan
Lafiya: Naira triliyan 2.48 tiriliyan
Tinubu ya bayyana kasafin da taken “Kasafin Haɗin Kai, Sabuwar Juriya da Rabon Arziki ga Kowa”, yana mai cewa kasafin ba wai takardun lissafi bane kaɗai, “bayyana fifikon ƙasa ne,” tare da alƙawarin dorewar kuɗi, gaskiya a bashi, da kashe kuɗi bisa ƙima.


