Gwamnatin tarayya ta bayyana rashin goyon bayan ta ga ƙudirin da ke gaban Majalisar Dattawa na gyara dokar yaƙi da ta’addanci, wanda ke neman sanya hukuncin kisa ga masu sace mutane.
Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN), ya ce saka hukuncin kisa a cikin doka na iya jawo matsaloli masu yawa, musamman a fannin haɗin gwiwar ƙasashen duniya wajen yaƙi da ta’addanci da manyan laifuka.
A cewar sa, ƙasashe da dama da Najeriya ke hulɗa da su na ƙalubalantar hukuncin kisa, kuma hakan na iya sa su ƙi miƙa wa Najeriya masu laifi da ake nema, idan har suna fuskantar barazanar hukuncin kisa.
> “Dole ne mu yi la’akari da illolin da saka hukuncin kisa zai haifar, musamman yadda zai iya kawo cikas ga haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa,” in ji Fagbemi.
Ministan ya ƙara da cewa, wannan mataki na iya bai wa manyan masu laifi mafaka a ƙasashen waje, domin kotunan can za su iya hana wa a mayar da su Najeriya bisa hujjar kare haƙƙin ɗan’adam.


