Majalisar Wakilai ta yi doka mai tsauri ga Masu Aikata Laifukan Zaɓe

0
9

Majalisar Wakilai ta yi doka mai tsauri  ga Masu Aikata Laifukan Zaɓe

Majalisar Wakilai ta amince da tsauraran matakai domin ƙarfafa hukunta laifukan zaɓe, bayan da ta yi wa Dokar Zaɓe ta shekarar 2022 kwaskwarima.

A zaman majalisa da aka gudanar ranar Alhamis, ‘yan majalisar sun amince da hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari ko tarar Naira miliyan 75 ga duk wanda aka samu da laifin ƙirƙirar takardun tsayawa takara ko lalata takardun sakamakon zaɓe. 

Wannan sabon hukunci ya fi na baya tsauri, inda a baya tarar ta kasance Naira miliyan 50.

Haka kuma, majalisar ta amince da tarar Naira miliyan 5 ga duk wanda ya yi amfani da katin zaɓe (PVC) ta hanyar da ba ta dace ba.

Sai dai, majalisar ta ƙi wani ƙuduri da ke neman kakabawa masu bai wa wakilai kuɗi ko kayan tallafi domin samun rinjaye wajen zaɓen jam’iyya hukuncin shekaru biyu a gidan yari. ‘Yan majalisar sun bayyana damuwa cewa irin wannan doka na iya zama hanyar cin zarafin ‘yan siyasa daga abokan hamayya.

Da yake bayyana dalilan sauye-sauyen, Shugaban Kwamitin Majalisar kan Harkokin Zaɓe, Hon. Adebayo Balogun, ya ce an fara gabatar da Kudirin Dokar Zaɓe ta 2025 ne da nufin sauya dokar gaba ɗaya, amma tsarin majalisa ya sa aka koma gyara maimakon soke dokar baki ɗaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here