Babu ministan da zai sha wutar lantarki kyauta a Afirka ta Kudu – Ramaphosa

0
98

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa yace daga yanzu babu wani ministan kasar da zai sha wutar lantarki ko ruwan sha kyauta kamar yadda aka saba a shekarun da suka gabata.

Wannan ya biyo bayan korafin da jama’ar kasar keyi akan yadda jami’an gwamnati ke samun ganima, yayin da sauran jama’a ke fama da karancin wutar lantarkin da kuma tsadar rayuwa.

Mai magana da yawun shugaban Vincent Magwenya, yace Ramaphosa yaji koke kokensu akan lamarin, kuma ya dauki matakin gyara domin daidaita al’amura lura da halin da ake ciki.

Kasar Afirka ta Kudu na daya daga cikin kasashen Afirka dakke fama da tsadar rayuwa, duk da kasancewar ta daya daga cikin wadanda suka fi habakar tattalin arziki a nahiyar.

A makonnin da suka gabata, kasar ta fuskanci katsewar wutar lantarkin wanda ya kaiga hana shugaba Ramaphosa tafiya Amurka taron Majalisar Dinkin Duniya.