Tsohon gwamnan Jihar Sakkwato, Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya sanar da komawa jam’iyyar APC.
Bafarawa ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, yayin wani taro da ya gudana a babban ɗakin taro na gidan sa da ke Sakkwato, inda magoya bayan sa suka halarta domin shaida musu inda ya koma a siyasan ce.
Tsohon gwamnan ya jaddada cewa ya daina siyasar neman kujera, kuma ba shi da niyyar tsayawa takarar neman kowane muƙami. Sai dai ya ce burin sa shi ne ganin magoya bayansa sun samu nasara a harkar siyasa.
A baya dai Bafarawa, ya kasance a cikin tafiyar jam’iyyar PDP kafin sanar da ficewa daga cikin ta.


