Farashin man fetur ya fara raguwa a sassan Najeriya bayan da matatar Dangote ta rage farashin man da Naira 125.
Sai dai duk da wannan sauƙin, yawancin gidajen mai har yanzu ba su saukar da farashin ƙasa da Naira 800 kan kowace lita ba.
A jihar Lagos, manyan ’yan kasuwa na sayar da fetur tsakanin Naira 820 zuwa Naira 890 kan lita, inda a baya ake sayarwa a Naira 910 zuwa Naira 920. Sai dai gidajen mai na MRS ne kaɗai ke sayar da fetur a kan Naira 739 kan lita, lamarin da ya haddasa dogayen layuka a wasu gidajen man, musamman a yankin Alapere.
Rahotanni sun nuna cewa matatar Dangote ta aiwatar da rage farashin ne a karshen mako, inda shugaban kamfanin, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa gidajen mai da ke ɗaukar fetur daga matatar za su fara sayarwa a Naira 739 a Lagos.
Masana sun ce wannan sauyin zai ƙara sanya gasa a tsakanin yan lasuwar mai, kuma ana sa ran ƙarin ragi musamman a lokacin bukukuwan ƙarshen shekara.
A Abuja kuwa, farashin fetur har yanzu yana sama da Naira 900 kan lita, yayin da farashin a Bayelsa ya sauka zuwa Naira 890.
A jihar Kano, rahotanni sun nuna cewa manyan ’yan kasuwa sun rage farashin fetur ɗin zuwa Naira 850 kan lita.


