Najeriya ba ta samu kuɗaɗen shigar da ta yi hasashen tattarawa ba –Gwamnatin tarayya

0
9

Ministan Kuɗi Wale Edun, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba ta cika burin ta ba wajen samun kuɗaɗen shigar da take son samu na shekarar 2025, sabanin abin da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana a baya, cewa an samu abin da ake buƙata.

Edun ya ce daga cikin Naira triliyan 40.8 da aka yi hasashen samu a 2025, gwamnati ta samu kimanin Naira triliyan 10.7 kawai, lamarin da ke nuna samun gagarumin giɓi a fannin kuɗaɗen shiga.

Ministan ya bayyana hakan ne a zaman tattaunawa da Kwamitocin Majalisar Wakilai kan Kuɗi da Tsare-tsaren Ƙasa, yayin nazarin Tsarin Kuɗaɗen Shekara (MTEF) da Takardar Dabarun Kuɗi (FSP) na 2026–2028 da Shugaban Ƙasa ya aike wa majalisar.

A cewarsa, kasafin 2025 na Naira triliyan 54.9, wanda aka kira kasafin farfaɗo da tattalin arziƙi, ya dogara da hasashen kuɗaɗen shiga na Naira triliyan 40.8, sai dai ba’a samu yadda ake so ba.

Edun ya danganta gibin da, raunin samun kuɗaɗen mai da gas, musamman harajin ribar man fetur da harajin kamfanonin mai, da kuma gazawar wasu hanyoyin samun kuɗi da ba na mai ba.

Har ila yau, ya ce domin cike giɓin, gwamnati ta karɓi bashin kusan Naira triliyan 14.1 tiriliyan.

Tun da farko, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa Najeriya ta cika burin ta a fannin samun kuɗaɗen shiga na 2025 tun a watan Agusta, kuma ƙasar ba za ta ƙara dogaro da bashi ba, kalaman da bayanan Ministan Kuɗi suka saɓa musu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here