Hukumar Binciken Hatsarurrukan Sufurin Jiragen Sama ta Ƙasa (NSIB) ta tabbatar da faruwar hatsari da ya shafi wani jirgin Cessna 172 mallakin kamfanin Skypower Express a Filin Jirgin Sama na Sam Mbakwe, Owerri, jihar Imo.
Sanarwar da daraktar hulɗa da jama’a ta NSIB, Bimbo Oladeji, ta fitar ta ce jirgin mai lambar rajista 5N-ASR ya taso daga Kaduna zuwa Port Harcourt, sai dai matuƙan jirgin suka sanar da uzurin gaggawa a sararin sama, inda suka karkata zuwa Owerri.
Rahotanni sun nuna cewa hatsarin ya faru ne da misalin 8:00 na daren Talata yayin saukar jirgin, inda ya yi saukar gaggawa tare da kifewa. Mutane huɗu ne ke cikin jirgin a lokacin da lamarin ya faru, kuma duk an kai su asibiti domin samun kulawa, amma babu rahoton mutuwa a hatsarin.
NSIB ta ce an gaggauta gudanar da ayyukan ceto, babu gobarar da ta tashi bayan hatsarin, kuma ba a dakatar da zirga-zirgar jirage a filin jirgin ba, domin sauran jirage sun ci gaba da sauka da tashi lafiya.


