Majalisa ta Amince da Naɗin Jakadun Najeriya

0
20

Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin jakadu uku na farko da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya aike mata domin wakiltar ƙasar Najeriya a ƙasashen waje.

Jakadun da aka amince da su sun haɗa da Aminu Muhammad Dalhatu daga Jihar Jigawa, Lateef Kayode Kolawole Are daga Jihar Ogun, da kuma Emmanuel Ayodele Oke, CFR, daga Jihar Oyo.

Amincewar ta biyo bayan gabatar da rahoton Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Waje, wanda ya gudanar da tantancewar waɗanda aka gabatar a makon da ya gabata, inda aka gamsu da cancantar su.

Sai dai Majalisar ba ta kai ga tabbatar da naɗin sauran jakadu 64 da Shugaba Tinubu ya aike mata ba, duk da cewa an riga an tantance su.

Shugaban Ƙasa ya miƙa sunayen jakadu ukun ne a ranar 26 ga Nuwamba, kuma wannan ne karo na farko da ya tura jerin sunayen jakadu zuwa Majalisar Dattawa tun bayan hawan sa mulki a ranar 29 ga Mayun 2023.

Wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na ƙarfafa dangantakar diflomasiyya tsakanin Najeriya da sauran ƙasashen duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here