Wasu daga cikin al’ummar Jihar Sokoto sun koka kan yadda tsadar kudin hayar gidaje ke kara ta’azzara, lamarin da suke cewa yana jinkirta aure tare da kara damuwa a zukatan matasa, musamman masu shirin yin aure.
Bincike ya nuna cewa matsalar gidaje ta sanya hayar gida ta wuce karfin yawancin samari masu niyyar aure, inda samun matsuguni ya zama babban cikas a jihar.
A shafukan sada zumunta, matasa mata da dama sun rika bayyana damuwarsu, suna cewa duk da sun shirya aure, samarin su sun gaza biyan kudin hayar wajen zama.
Wani dillalin gidaje, Alhaji Murtala Falke, ya ce hatta mafi saukin gida yanzu ya fi karfin talakawa.
“Daki guda yana kaiwa kusan naira 300,000 a shekara, yayin da farashin hayar ƙaramin gida ke farawa daga naira 400,000 zuwa sama. Gidan dakuna biyu kuma na kaiwa tsakanin naira miliyan 1.5 zuwa miliyan 2 a shekara,” in ji shi.
Alhaji Ahmed Falke, ya danganta matsalar da tsadar kayan gini da karancin gine-ginen zama.
“Buhun siminti yanzu yana kusan naira 9,000, fili kuma da a da naira miliyan 3 ake saya, yanzu ya haura naira miliyan 12,” in ji shi.
Daraktan Hisbah na Jihar Sokoto, Malam Nura Attahiru, ya bayyana cewa matsalar ta shafe shi kai tsaye.
“Ina da ’ya’ya biyu da suka shirya aure, amma ban samu gidan da zan zaunar da su ba, duk da biyan fiye da naira miliyan 1.3,” in ji shi.
A martanin ta, Gwamnatin Jihar Sokoto ta ce tana gina sama da gidaje 1,000, yayin da Gwamnatin Tarayya ke gina wasu gidaje 250 karkashin shirin Renewed Hope Agenda.


