Ministan Sadarwa da Kirkire-kirkire, Bosun Tijani, ya bayyana cewa ’yan bindiga na amfani da fasaha ta musamman wajen yin kiran waya domin gujewa sa ido da bin sawu daga jami’an tsaro.
Ministan ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na tashar talabijin ta Channels a daren Juma’a.
A cewar sa, bin diddigin kiran wayar da yan bindiga ke yi yana da wahala fiye da yadda mutane da dama ke zato.
> “Ba sa amfani da hanyar sadarwa ta yau da kullum,, in ji Tijani.
Ministan ya ce hakan ne ya sa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci a zuba jari sosai wajen gina hanyoyin sadarwa a yankunan da ke fama da matsalar tsaro.
Ya kuma ƙara da cewa gwamnatin tarayya na shirin inganta tauraron dan adam domin ƙarfafa sa ido da tattara bayanan tsaro.


