Hukumar EFCC ta kama tsohon ƙwadago Ngige

0
10

Hadimin tsohon Gwamnan Jihar Anambra kuma tsohon Ministan Kwadago, Dr. Chris Ngige, Fred Chukwuelobe, ya tabbatar cewa Ngige, yana hannun Hukumar EFCC, ba a sace shi aka yi ba kamar yadda aka ruwaito ba a baya.

A daren Litinin ne aka yaɗa labarin cewa an yi garkuwa da Ngige, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce. 

Sai dai a cikin wata sanarwa da Chukwuelobe ya wallafa, ya ce mutane da dama suna kiran sa suna neman jin gaskiyar al’amarin, don haka ya bayyana cewa:

“Ngige yana hannun EFCC. Ba a sace shi ko garkuwa da shi ba.”

Sai dai kakakin EFCC, Dele Oyewale, bai amsa kira ko sakon da aka aike masa ba domin samun tabbacin hakan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here