A ranar Larabar data gabata ne Najeriya da Saudiyya suka sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya ta tsaro, wacce za ta ƙarfafa haɗin gwiwa a fannonin soja, horo, musayar bayanan sirri da ayyukan haɗin gwiwa.
Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ne ya wakilci Najeriya, yayin da Dr. Khaled H. Al-Biyari ya wakilci Saudiyya.
Matawalle ya ce yarjejeniyar “muhimmin mataki ne” da zai ƙara inganta ayyukan tsaro a Najeriya.
Yarjejeniyar na zuwa ne a lokacin da Najeriya ke fama da satar ɗalibai, hare-haren ’yan bindiga, da barazanar Boko Haram da ISWAP a arewa.
Za a aiwatar da yarjejeniyar na tsawon shekara biyar kafin a sake duba ta, kuma kowace ƙasa na iya janyewa daga yarjejeniyar bayan wa’adin wata uku.
Masana irin su Dr. Riyauddeen Zubairu Maitama, sun ce haɗin gwiwar zai fi tasiri wajen yaƙi da ta’addanci, kasancewar Saudiyya na cikin ƙasashen da ke yin babban aiki a wannan fanni.


