Fitaccen marubuci Farfesa Wole Soyinka, ya kalubalanci matakin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na tura dakarun sojin Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin bayan yunƙurin juyin mulkin da aka yi a ƙasar.
Yayin bikin bayar da kyaututtuka na shekara ta 20 da Cibiyar Binciken Kwakwaf ta Wole Soyinka (WSCIJ) ta shirya a Legas, Soyinka ya ce Tinubu bai kamata ya yi gaggawar aika sojoji, makamai da kayan yaƙi zuwa Benin ba, musamman ganin cewa akwai hanyoyi daban na magance rikicin.
Ya ce ya yi mamakin yadda ake girke manyan jami’an tsaro wajen gadin ɗan shugaban ƙasa, Seyi Tinubu, lamarin da ya ce ya isa ya tsare ƙasar Benin gaba ɗaya.
Soyinka ya ba da misali da wata ziyara da ya kai Legas kwanaki kaɗan da suka gabata, inda ya ce ya tarar da jami’an tsaro kusan 15 dauke da manyan makamai suna gadin Seyi a wani otel da ke Ikoyi.
A cewarsa, “Idan akwai wanda za a tura Benin domin kwantar da tarzoma, to Seyi ya fi dacewa, tunda rundunar tsaro da ke gadin sa ma ta isa ta kare ƙasar Benin.
Ya ƙara da cewa tura sojojin Najeriya zuwa Benin kan rikicin cikin gida ba lamari ne da ya dace da ka’idojin ƙasa da ƙasa ba, balle ma tsarin tsaron Najeriya na cikin gida.
Soyinka ya yi nuni da cewa Tinubu ba shi ne shugaban ƙasa na farko da yake da ’ya’ya ba, amma bai kamata a tsare manyan jami’an tsaro wajen gadin ɗan sa ba, alhali akwai manyan matsalolin tsaro da ke bukatar kulawa a ƙasar.


