Jami’ar Bayero ta sanar da ranar bude makaranta

0
112

Biyo bayan dakatar da yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’in ASUU ta yi na wata 8, daraktan hulda da jama’a na jami’ar ya ce jami’ar za ta dawo da harkokin karatu daga ranar 24 ga watan Oktoba.

A wata sanarwa da mataimakin magatakardar mai kula da harkokin jama’a Lamara Garba Azare ya fitar, ya ce an amince da ci gaba da aikin ne bayan ganawar da jami’ar ta yi a ranar 13 ga watan Oktoba.