Tsohon gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ja kunnen ’yan jam’iyyar APC da su daina fitowa suna ayyana wani mutum a matsayin dan takarar gwamnan Kano a zaben 2027 tun da lokaci bai yi ba.
Wasu jiga-jigan jam’iyyar sun fara nuna goyon baya ga mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, suna cewa shi ne ya kamata ya tsaya takara. Sai dai Ganduje ya ce irin wannan gaggawar na iya haifar da rarrabuwar kai a cikin jam’iyya.
Daga cikin wadanda suka fara kiran Barau ya tsaya takara, Baffa Takai ya janye maganarsa, inda ya nemi afuwar ’yan jam’iyya.
A yayin wata ganawar sa da BBC, Ganduje ya ce dole a bari lokacin tantance ’yan takara ya yi, sannan a zabi wadanda suka dace ba tare da tayar da fitina ba. A cewarsa, shugabannin jam’iyya a Kano suna jiran jagorancinsa don daidaita alkiblar da za a bi, amma har yanzu ana samun masu gaggawar ayyana gwanayensu.


