Jami’an ’yan sanda sun kai samame zuwa ofishin Barrister Muhuyi Magaji Rimingado, tsohon shugaban Hukumar Karɓar da Korafe-korafe da Yaki da Cin Hanci ta Jihar Kano, inda suka kama shi tare da tafiya da shi.
Shaidun gani da ido sun ce jami’an sun bayyana kansu a farko cewa daga sashen bincike na CID suka fito. Sai dai da aka isa hedikwatar ’yan sanda da ke Bompai, an bayyana cewa kamun ya fito ne bisa umarnin Babban Sufeton ’Yan Sanda na Ƙasa, Kayode Egbetokun.
Rahotanni sun ce an shirya kai Muhuyi zuwa Abuja domin ci gaba da bincike.


