An kai hari a taron PDP na Kaduna

0
94

Hankula sun tashi a filin wasa na Ranches Bees, harabar da jam’iyyar PDP ta gudanar da gangamin yakin neman zaben dan takararta na Shugaban Kasa, Atiku Abubakar.

Lamarin dai ya wakana ne yayin da wasu da ake kyautata zaton ’yan barandan siyasa ne sun kai hari kan magoya bayan jam’iyyar ta PDP a ranar Litinin din nan.

Aminiya ta ruwaito cewa, mahalarta taron dai sun rika neman mafaka yayin da ’yan barandan dauke da adduna sauran makamai iri-iri suka rika jifan mutane da duwatsu.

Haka kuma, an ruwaito cewa, ’yan daban sun yi wa jama’a da dama kwacen wayoyinsu na salula yayin taron.

Tuni dai tsohon Mataimakin Shugaban Kasar Atiku ya yi martani kan wannan lamari da ya bayyana a matsayin abu takaici daga masu adawa da jam’iyyar PDP.

Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Atiku ya yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya gargadin magoya bayan sauran jam’iyyu da su shiga taitayinsu.

Atiku wanda ya tunatar da yadda suka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da tabbatar da aminci yayin yakin neman zabe, ya ce aukuwar wannan lamari a yanzu ya saba wa tsari na dimokuradiyya.

“Ina kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya ja hankalin dukkan magoya bayan jam’iyyu da su yi taka tsan tsan kan alkawarin tabbatar da zaman lafiya da suka dauka,” a cewar Atiku.

Mai Magana da Yawun rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Muhammad Jalige, ya ce tuni sun tura jami’ansu harabar domin kwantar da tarzoma.