Gwamnatin Kano Za Ta Gina Sabbin Gidaje 1,800

0
9

 

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa tana shirin gina sabbin gidaje na zamani guda 1,800 a kananan hukumomi 36 na jihar, a wani yunkuri na inganta rayuwar al’umma a yankunan karkara.

Kwamishinan Ma’aikatar Gidaje, Arc Ibrahim Yakubu Adamu, ne ya bayyana hakan yayin ganawar da ya yi da tawagar gwamnatin jihar Jigawa a ofishinsa. Ya ce kowacce karamar hukuma za ta samu rukunin gidaje 50 tare da muhimman abubuwan more rayuwa.

Arc Adamu ya ce wannan shiri na daga cikin alkawuran da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dauka na samar da ingantattun gidaje, ciki har da makaranta, ofishin ’yan sanda, asibiti, ruwan sha da wutar lantarki domin tabbatar da cewa sabbin unguwannin da za’a samar za su kai wani babban mataki.

Kwamishinan ya kuma sanar da cewa fiye da kamfanonin gine-gine 100 ne suka nemi shiga hadin gwuiwa da gwamnati, inda akalla 60 daga cikin su ciki har da na cikin gida da na kasashen waje aka zaɓa domin duba yiwuwar aiki tare wajen samar da gidaje masu inganci da rahusa a jihar Kano.

Shugaban tawagar gwamnatin Jigawa, Abdullahi Hassan, wanda kuma shi ne Babban Sakataren Ma’aikatar Ƙasa, Gidaje da Tsare-tsaren Birane ta jihar, ya ce sun zo Kano ne domin nazari da koyo daga ayyukan da ake yi a ma’aikatun jihar. Ya yabawa gwamnatin Kano bisa gagarumin ci gaban da ake samu a bangaren gine-gine.

Ya kuma bukaci gwamnati ta ci gaba da karfafa zumunci da hadin kai tsakanin jihohin biyu, kamar yadda daraktan faɗakarwa na ma’aikatar Adamu Abdullahi, ya sanar cikin wata sanarwa ya fitar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here