Wani kamfanin ƙasar Amurka ya janye daga dillancin jirgin fadar shugaban Najeriya

0
8

Kamfanin JetHQ na ƙasar Amurka, da ke gudanar da tallace-tallacen jiragen sama a duniya ya janye hannun sa  daga sayar da jirgin fadar shugaban ƙasar Najeriya ƙirar Boeing 737-700, wanda gwamnatin Tarayya ta sanya a kasuwa tun watan Yulin 2025.

Binciken da jaridar Punch, ta gudanar gano cewa jirgin wanda a a baya ke cikin jerin kayayyakin da kamfanin ke dillanci, yanzu an cire shi daga shafin kamfanin.

Manajan kamfanin , Laurie Barringer, ya tabbatar da cewa a halin yanzu basu da hannu a cinikin jirgin.

Sai dai har yanzu ba a samu martanin mai magana da yawun Ofishin Mai Bawa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro, Ismail Garba, ba, duk da alƙawarin da ya yi a kan yin ƙarin haske dangane da hakan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here