Ba za a sake yin sulhu ko biyan kuɗin fansa ga ‘yan ta’adda ba–Christopher Musa

0
8

Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya ce gwamnati ba za ta kara tattaunawa ko biyan kudin fansa ga ‘yan ta’adda ba saboda hakan na ƙara musu ƙarfin gwiwa da damar kai sabbin hare-hare. 

Ya yi wannan bayani ne yayin tantancewar da aka yi masa a majalisar dattawa, inda ya jaddada bukatar gano masu aikata laifin ta’addanci da dakile shi.

Ya kuma yi kira a hanzarta shari’ar ‘yan ta’adda, yana mai cewa jinkirin shari’a na rage wa jami’an tsaro kwarin gwiwa.

A gefe guda, Majalisar Wakilai ta bukaci gudanar da shari’ar ‘yan ta’adda a bainar jama’a, tare da kare shaidu, da kuma aiwatar da sabbin shawarwari kan tsaro ciki har da fasahar leken asiri, ƙarin jami’an tsaro, gyaran dokoki da ingantaccen hadin gwiwar kasa da kasa.

Majalisar Dattawa kuma ta fara gyaran dokar ta’addanci domin sanya hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane, masu daukar nauyin su da masu ba su bayanai. 

Ministan Tsaron ya kuma bayyana shirin cire sojoji daga shingayen tituna domin mayar da su cikin dazuzzuka, tare da tabbatar da tsaro ga manoma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here