Ƴan siyasa ne ke rura wutar ta’addanci a arewa—Irabor

0
22

Tsohon hafsan hafsoshin tsaron ƙasa Janar Lucky Irabor (mai ritaya), ya bayyana cewa akwai ’yan siyasar da ke daukar nauyin hare-haren ƴan ta’adda da ake yi don cimma wasu manufofin siyasa.

A baya ma, mashawarcin shugaban kasa Daniel Bwala ya ce gwamnati na shirin fallasa sunayen masu daukar nauyin ayyukan ta’addanci. Masana tsaro sun tabbatar da cewa akwai gaskiya a irin wadannan zarge-zarge, musamman a yankunan Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.

A hirar sa da Channels TV, Irabor ya ce akwai jami’ai a gwamnati da ke nuna suna yaki da ta’addanci, amma su ne ke taimakawa wajen haddasa tashin hankali.

Masu ruwa da tsaki sun bukaci gwamnati ta fallasa sunayen ’yan siyasar da ake zargi, musamman a wannan lokaci da hare-haren ’yan bindiga suka karu a jihohin Arewa.

Wannan na faruwa ne yayin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatar da dokar ta-baci a bangaren tsaro, tare da sauya Ministan Tsaro daga Muhammad Badaru Abubakar zuwa Janar Christopher Musa (mai ritaya), wanda ke jiran amincewar Majalisar Dattawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here