‘Yan bindiga sun afka kauyen Unguwar Tsamiya na Faruruwa da kuma Dabawa, duka a cikin ƙaramar hukumar Shanono ta Jihar Kano, inda suka yi garkuwa da akalla mutum 25 tare da jikkata wasu biyu.
Harin ya faru a daren Lahadi, kasa da awanni 24 bayan wani hari makamancin haka a Yan Kamaye da ke Tsanyawa, wani yanki da ke iyaka da Jihar Katsina.
Wani masani kan rikice-rikice da tsaron yankin Arewa maso Yamma, Bakatsine, shi ne ya fitar da bayanan harin a ranar Litinin. Ya tabbatar da cewa maharan sun kutsa cikin al’ummomin ne da dare, inda suka yi awon gaba da mazauna kauyukan ba tare da wani jinkiri ba.
Ya kuma yi tambaya kan tasirin yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla da ‘yan bindiga a Jihar Katsina, musamman a kananan hukumomin da ke iyaka da Kano, duba da yawaitar hare-haren da ake sake fuskanta.
Hare-haren da suka biyo a jere a makonnin nan sun kara tada hankalin jama’a, musamman mazauna yankunan arewacin Kano da ke iyaka da Katsina.


