Karamin ministan tsaro Bello Mohammed Matawalle, ya musanta wani rahoton da ya bazu a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa ya ce shawo kan rashin tsaro a Zamfara “ba za su yi tasiri ba idan ba tare da shi ba.”
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, Matawalle ya bayyana labarin a matsayin ƙarya da yaudara, yana mai cewa bai taɓa faɗa ko bayar da irin wannan bayani ba.
Ya ce duk da cewa ya saba nuna damuwar sa kan matsalar tsaro a jihar, bai yi wata hira ko magana da ke nuni da cewa nasarar rundunonin tsaro tana dogara da shi ko tasirin sa ba. Ministan ya kara da cewa irin wannan ƙarairayi na iya tada hankula da haifar da rikice-rikice marasa amfani.
Matawalle, wanda tsohon gwamnan Zamfara ne, ya bayyana cewa dukkan maganganun sa a baya sun ta’allaka ne kan bukatar haɗin kai tsakanin Gwamnatin Tarayya, jihohi da hukumomin tsaro domin samun dawwamammen zaman lafiya.
Ya kuma ja hankalin ’yan jaridu da sauran kafafen yada labarai da su rika tabbatar da sahihancin bayanai kafin wallafawa, musamman ma kan batutuwan tsaro da ke bukatar kulawa ta musamman.


