Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci makiyaya su dakatar da kiwon sakin dabbobi, su kuma mika dukkan makamai marasa lasisi da suka mallaka, tare da komawa tsarin kiwon zamani na domin kawo ƙarshen rikicin manoma da makiyaya.
A wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar a ranar Laraba, Tinubu ya ce gwamnati na daukar matakai na dindindin don shawo kan rikice-rikicen da suka addabi arewa musamman a yankunan Arewa ta Tsakiya.
Wannan umarni na zuwa ne a daidai lokacin da sace-sacen ɗalibai suka ƙaru a jihohin Niger, Kebbi da wasu sassa na ƙasar, haka kuma hare-haren da ake samu tsakanin manoma da makiyaya sun yi sanadin mutuwar mutane da dama a watannin baya-bayan nan.
Shugaban ya kuma umarci masallatai da coci-coci, musamman a yankunan da ake fama da rikice-rikice, da su yi aiki tare da jami’an tsaro domin kare al’umma yayin salla da taruka.
Ya ce kirkirar Ma’aikatar Kiwon Dabbobi muhimmin bangare ne na tsarin gwamnati na tsawon lokaci, domin inganta harkar kiwo da samar da zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya.


