Sanatoci sun soki umarnin janye yan sanda daga maga manyan mutane, sun ce rayukan su na cikin haɗari
Wasu ƴan majalisar dattawa sun yi gargadi cewa umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na janye jami’an ‘yan sanda daga manyan mutane ya zo a “mummunan lokaci,” yana barin su cikin hatsarin hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane.
Sanata Aliyu Wamakko da Sanata Tahir Monguno sun ce ‘yan siyasa na kara zama manyan manufofin miyagu, musamman yayin ziyartar mazabu, don haka janye masu tsaro zai iya haifar da mummunar illa. Majalisar Dattawa ta yanke shawarar tunkarar Shugaban Kasa da hukumar ’yan sanda domin sake duba matakin.
A Majalisar Wakilai, Ahmed Idris Wase ya yi gargadin cewa ‘yan siyasa da jami’an gwamnati na fuskantar barazana kai tsaye, musamman ganin yadda garkuwa da mutane ke ƙaruwa a manyan hanyoyi.
Majalisar Dattawa ta kuma amince da kudurin da zai mai da garkuwa da mutane laifin ta’addanci tare da hukuncin kisa, bayan rahotannin da ke nuna karin rashin tsaro a jihohin Kebbi, Niger da Kwara.
Sanatocin sun kuma duba yiwuwar bai wa ‘yan kasa nagari damar mallakar bindiga domin kare kai, yayin da Mataimakin Shugaban Majalisa, Barau Jibrin, ya bukaci karin hadin kai tsakanin jihohi da gwamnatin tarayya wajen yaki da ta’addanci.


