Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci kan sha’anin tsaro

0
9

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya ayyana dokar ta-ɓaci kan tsaro a fadin ƙasar nan, tare da bada umarnin ɗaukar karin jami’an tsaro domin magance ta’addanci da rashin tsaro da ya addabi sassa daban-daban na Najeriya.

A cikin jawabin da ya gabatar a fadar gwamnati, Tinubu ya ce rundunar ‘yan sanda za ta ɗauki sabbin karin jami’ai 20,000, wanda hakan ya kai adadin jami’an da ake shirin ɗauka zuwa 50,000, bayan umarnin baya da ya bayar na ɗaukar 30,000.

Mai taimakawa shugaban ƙasa a fannin yaɗa labarai, Abdulaziz Abdulaziz, ya shaida wa BBC cewa ayyana dokar ta-ɓacin na nufin hanzarta ɗaukar matakan gaggawa domin farfado da tsaro a duk fadin Najeriya.

Haka kuma, shugaban ya bai wa hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) umarnin ɗaukar karin ma’aikata a rundunar kare dazuka (Forest Guard) da kuma tura su nan take zuwa dazukan da ‘yan ta’adda ke ɓoye.

Tinubu ya ce DSS na da cikakken izini na “fatattakar ‘yan ta’adda da miyagu daga dukkan dazuka”, yana mai cewa:

“Ba za a sake samun inda miyagu za su ɓuya ba.”

Wannan mataki na zuwa ne a lokacin da hare-haren ta’addanci, garkuwa da mutane, da fashi da makami suka yi ƙamari a jihohi da dama, wanda hakan ya tilasta gwamnati ɗaukar tsauraran matakai don dawo da zaman lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here