Tinubu ya turawa majalisar dattawa sunan mutanen da zai naɗa a matsayin jakadu
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya aika da jerin sunayen mutane uku da yake son a tabbatar wa a matsayin jakadu zuwa Majalisar Dattawa.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya karanta sunayen a zaman majalisar na ranar Laraba.
Masu jiran tabbatarwar su ne:
- Kayode Are
- Aminu Dalhatu
- Ayodele Oke
Akpabio ya ce wannan jerin farko ne, yana mai cewa akwai yiwuwar ƙarin sunaye su biyo baya.
A halin yanzu ba a fitar da cikakken bayani kan inda za a tura su ba.


