Kasashe 5 da ba su da ‘Yan Sanda Da Gidajen Yari 

0
6

A duk duniya ana tsammanin kowace kasa tana da hukumomin tsaro da kuma gidajen gyaran hali domin tabbatar da doka da ka’ida. 

Sai dai wasu ƙananan ƙasashe suna gudanar da mulkin su ba tare da irin waɗannan manyan tsarin ba, saboda ƙarancin yawan jama’a da kuma alakar da suke da ita da maƙwabtan su.

Ga jerin waɗannan ƙasashe:

1. Vatican City

Vatican ita ce ƙaramar ƙasa a duniya. 

Duk da cewa tana da ƙungiyar tsaro ta Gendarmerie da masu tsaron fadar Paparoma, ba ta da kurkukun dogon zama. 

Mutanen da aka yanke wa hukuncin daurin shekaru ana mika su Italiya bisa yarjejeniya. Su kan tsare mutum na ɗan lokaci kaɗan kawai.

2. Monaco

Monaco ƙasa ce mai arziki da ƙarancin yawan jama’a. Duk da tana da rundunar ‘yan sanda mai ƙarfi, ba ta da babban gidan yari. Masu laifin daurin dogon lokaci ana mika su Faransa.

3. Liechtenstein

Liechtenstein ƙaramar ƙasa ce sosai, hakan yasa ba ta buƙatar manyan gidajen yari. Tana da ɗan ƙaramin wurin tsarewa na wucin gadi, amma idan an yanke hukuncin dogon zama, ana tura wanda abin ya shafa Switzerland, ƙasar da take da alaƙa ta siyasa da zamantakewa sosai da ita.

4. San Marino

San Marino, duk da kasancewar ta tsohuwar jamhuriya, tana da ƙananan hukumomin tsaro ba tare da babban gidan yari ba. Ana tsare mutum na ɗan lokaci kawai, sannan manyan laifuka ana mika su Italiya domin cigaba da zaman gidan gyaran hali.

5. Andorra

Andorra da ke tsakanin Spain da France ta dade tana dogaro da waɗannan ƙasashe wajen tsare masu manyan laifuka. Tana da ƙaramin wurin tsarewa, amma idan an yanke hukuncin dogon zama, ana tura mutum Spain ko France.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here