An samu nasarar ceto dalibai mata 24 na Makarantar Sakandaren ’Yan Mata ta Gwamnati da ke Maga, Jihar Kebbi, waɗanda ’yan bindiga suka sace ranar 17 ga Nuwamba.
Majiyoyin tsaro sun tabbatar da ceton, duk da cewa cikakken bayani kan yadda aka aiwatar da aikin ceton bai fito ba.


