Yan Bindiga Sun Sace Mutane 18 a Kano

0
9

’Yan bindiga sun kai hari a kauyen Biresawa, dake karamar hukumar Tsanyawa a Kano, inda suka tsere da mutane 8 maza 2 da mata 6 da misalin ƙarfe 11 na dare ranar Litinin.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun shigo daga kauyen Tsundu, suna ɗauke da makamai, suka kuma yi awon gaba da mata da yarinya mai shekara 17. An ce mazauna yankin sun sanar da jami’an tsaro tun kafin harin, amma hakan bai hana faruwar lamarin ba.

An kuma kai hari a wasu kauyuka dake kusa da yankin, masu suna Sarmawa, Yan Chibi, da Gano, inda maharan kusan 50 suka shiga da babura, suka sace mutane sama da goma.

’Yan sa-kai da mazauna yankin sun bi sawun maharan, amma sun shiga Jihar Katsina.

Yanzu haka jama’a na rayuwa cikin tsoro, wasu mazauna sun bar gidajensu saboda yawan hare-haren da suka addabi yankin. Rundunar ’yan sanda ba ta fitar da bayani ba tukuna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here