Saudiya ta bayar da damar buɗe sabbin shagunan siyar da giya a ƙasar

0
28

Gwamnatin Saudiyya ta faɗaɗa damar samun barasa ga mazauna ƙasar waɗanda ba Musulmi ba, inda yanzu an ƙara yawan shagunan da ke sayar da ita a unguwannin da jami’an diplomasiya ke zaune a Riyadh. 

Matakin na zuwa ne a matsayin wani ɓangare na shirin VISION 2030 na Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman, wanda ke ƙoƙarin jawo hankalin masu yawon buɗe ido da zuba jari.

Rahotanni sun nuna cewa ma’aikatan ƙetare masu samun kaso mai tsoka na albashi za su iya saya da shan barasa karkashin kulawar gwamnati. Haka kuma, mazauna ƙetare da suka saba yin barasa a gidajensu yanzu za su iya neman lasisi na yin cinikin barasa a hukumance.

Sauye-sauyen suna daga cikin manyan matakai da Saudiyya ke ɗauka domin sassauta dokokin zamantakewa ciki har da buɗe sinima, bai wa mata damar tuƙi, da bunƙasa fannin yawon buɗe ido.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here