Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana cewa zai kasance a sahun gaba wajen neman a yi wa shugaban ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, afuwa idan har ya nuna nadama kan abubuwan da ya aikata a baya.
Gumi ya yi wannan bayani ne a cikin shirin The Morning Brief na talabijin ta Channels, a ranar Talata, inda ya ce Kanu na da damar neman sulhu muddin ya janye da kalaman da ke nuna komawa kan manufar sa ta baya.
Wannan furuci nasa na zuwa ne mako guda bayan wata babbar kotun tarayya a Abuja ta yanke wa Kanu hukuncin ɗaurin rai da rai, bayan ta same shi da laifuka bakwai da suka shafi ta’addanci. Daga nan aka mika shi zuwa Kurkukun Sokoto.
“In da Nnamdi Kanu, wanda aka daure bisa zargin ta’addanci da barazanar kashe sojoji, ya fito ya nuna nadama da kiraye-kirayen zaman lafiya, zan yi kira a yi masa afuwa da neman sassauci,” in ji Gumi.


