Al’ummar Yobe sun koka a kan yawaitar sace matattu daga kaburbura

0
13

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Yobe ta bayyana damuwa kan yawaitar lalata kaburbura da ake yi a wasu sassan jihar, tare da tabbatar da cewa tana ƙara ƙaimi wajen kamo masu aikata wannan mummunan laifi.

A ranar Litinin ne aka sake samun wani lamari a Potiskum, inda mazauna yankin suka sanar da ofishin ‘yan sanda cewa wasu da ba a san ko su waye ba sun shiga makabartar Nahuta suka tono kabarin wani ƙaramin yaro, sannan suka tsere da gawar.

Kakakin rundunar, SP Dungus Abdulkarim, ya bayyana cewa wannan ba shi ne karo na farko da irin wannan ta’asa ta faru ba, domin a farkon watan nan an samu makamancin lamarin a Karamar Hukumar Jakusko, inda bincike a kan wadanda ake zargi har yanzu ke ci gaba da gudana.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, CP Emmanuel Ado, ya yi tir da wannan danyen aiki, yana mai kiran sa da ta’addanci kuma abin takaici matuƙa.” Ya umarci a ƙara sanya ido, da ƙarfafa sintiri a makabartu, tare da tabbatar da cewa an kamo duk wanda ke da hannu a wannan laifi.

Rundunar ta kuma bukaci al’umma su kasance masu sa ido, tare da bayar da ingantattun bayanai da za su taimaka wajen gano masu aikata wannan ta’asa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here