ASUU ta bayyana lokacin yanke hukunci kan tafiya sabon yajin aiki

0
11

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ƙasa (ASUU) ta shirya gudanar da taron Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (NEC) a ranar Laraba domin yanke matsaya kan matakin da za ta ɗauka, bayan kammala sabbin tattaunawa da kwamitin sulhu na Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Yayale Ahmed.

A yunkurin dakile yiwuwar sabon yajin aiki, gwamnatin tarayya ta sake komawa teburin tattaunawa da ASUU a ranar Litinin, inda aka ci gaba da tattaunawar a daren jiya kuma ake sa ran kammala ta yau Talata.

Wani mamba na ASUU da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa tattaunawar ta ranar Litinin da Talata ita ce za ta fayyace matakin da ƙungiyar za ta ɗauka.

“Da zarar mun kammala a yau, kwamitin zartaswa zai zauna a gobe (Laraba) domin yanke hukunci. A wancan lokaci kowa zai ji sakamakon,” inji shi.

ASUU na zargin gwamnati da sakaci wajen cika muhimman bukatun ta da suka shafi inganta tsarin jami’o’i, alawus na malamai da sauran matsalolin da suka daɗe suna kai ruwa rana a kai.

Sai dai Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, wanda baya ƙasar nan a halin yanzu, ya dage cewa gwamnati ta kusan cika dukkan bukatun ƙungiyar. Ya kuma tunatar da cewa Shugaba Bola Tinubu ya umurce su da tabbatar da cewa ba a sake samun yajin aiki a jami’o’in gwamnati ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here