Majalisar wakilai za ta gudanar da zama na musamman kan tsaro

0
8

Majalisar Wakilai za ta gudanar da wani Zama na Musamman a ranar Talata, 25 domin tattaunawa kan matsalolin tsaro da suka addabi Najeriya da ƙarfafa matakan tsaro da ake ɗauka wajen magance su.

A wata sanarwa da mai magana da yawun majalisar, Hon. Akin Rotimi, ya fitar, an bayyana cewa zaman zai gudana ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Abbas Tajudeen, kuma an kebe shi ne domin nazari kan halin da ake ciki da kuma samun bayanai daga kwamitocin tsaro.

Rotimi ya ce wannan zama zai bai wa ‘yan majalisa damar tattauna matsalolin tsaro na mazabun su kai tsaye da kuma samar da mafita ta hanyar haɗin kai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here