Gwamnonin kudu maso yamma na gudanar da taro kan matsalolin tsaro

0
11

Gwamnonin kudu maso yamma na gudanar da taro kan matsalolin tsaro

Gwamnonin jihohin Kudu maso Yamma sun isa birnin Ibadan domin halartar wani taron gaggawa kan sha’anin tsaro sakamakon ƙaruwar matsalolin tsaro da ke tasowa a yankin.

Taron wanda za a gudanar a ofishin Gwamnan Oyo da ke Agodi, yana ƙarƙashin jagorancin Gwamna Seyi Makinde. Ana sa ran gwamnonin jihohin Lagos, Ogun, Oyo, Osun, Ondo da Ekiti za su halarta.

Majiyoyi sun bayyana cewa taron gaggawar na nufin tattauna barazanar tsaro da ta ƙaru a ‘yan kwanakin nan, inganta ayyukan haɗin gwiwar yankin, da kuma duba batutuwan ci gaban ababen more rayuwa a yankin.

Haka kuma, gwamnonin za su sake nazarin yadda ake tafiyar da rundunar tsaro ta Amotekun, tare da ɗaukar matakai wajen ƙarfafa ayyukan ta domin fuskantar ƙalubalen tsaro a zamanan ce.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here