Rahotanni daga yankin Dutsen Mandara na ƙaramar hukumar Gwoza, Jihar Borno, sun tabbatar da cewa mayakan Boko Haram tsagin Ali Ngulde sun kashe wasu mata biyu bayan zargin su da yin shirka.
Majiyoyin tsaro sun ce an kama matan ne a lokacin da ’yan kungiyar ke gudanar da bincike a yankin, inda suka samu layu a tare da su. A wani bidiyo da suka fitar, mayakan sun bayyana cewa wannan “shaida ce” ta aikata abin da suka kira haramtacciyar hanya.
Bayan kama su, an garzaya da matan zuwa wasu tsaunuka, inda aka yi musu kisa a bainar jama’a domin tsoratar da mazauna yankin da kuma tilasta su bin tsarin kungiyar.
Rahotanni sun kara nuna cewa bangaren Ali Ngulde ya tsaurara hukunci a watannin baya-bayan nan, inda ake kai farmaki ga jama’a kan zargin sihiri, leƙen asiri, ko kuma yunkurin guduwa daga yankunan da suke ƙarƙashin ikon su.


