Zulum ya bukaci al’ummar Borno su yi Azumi da addu’a kan matsalar tsaro

0
14

Zulum ya bukaci al’ummar  Borno su yi Azumi da addu’a kan matsalar tsaro

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi kira ga mazauna jihar da su tashi da azumi a yau Litinin domin neman taimakon Allah kan matsalolin tsaro da suka ta’azzara a jihar da kuma fadin Najeriya.

Gwamnan ya bayyana haka ne cikin wani faifan bidiyo da aka nada a harsunan Kanuri, Hausa da Turanci, inda ya bukaci jama’a su ci gaba da gode wa Ubangiji bisa irin nasarorin da jami’an tsaro suka samu a shekarun baya wajen dakile Boko Haram, tare da rokon su su kara dagewa da addu’o’i na musamman domin samun zaman lafiya.

Ya ce duk da irin nasarar da aka samu a baya, yanayin tsaro na ci gaba da sauyawa, lamarin da ya sa ya zama wajibi al’umma su hada kai wurin rokon Allah ya kawo ƙarshen kalubalen da ake fuskanta.

Borno dai ita ce cibiyar da rikicin Boko Haram ya fara tun a shekarar 2009, kafin daga bisani ya yadu zuwa wasu sassan arewacin Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here