Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, yana dab da bayyana komawar sa jam’iyyar ADC a hukuman ce a gobe Litinin, matakin da ake ganin zai iya sauya taswirar siyasar Najeriya nan gaba kaɗan.
Yayin da yake jawabi ga magoya baya da jiga-jigan jam’iyyar ADC a Jihar Adamawa, Atiku ya bayyana cewa zai yi rajista da jam’iyyar a ranar Litinin.
Ana sa ran wannan sauyin zai haifar da bayyana mabanbantan ra’ayi a jam’iyyun siyasa, musamman duba da tasirin Atiku a arewa da kuma shirin jam’iyyar ADC na faɗaɗa karfinta a matakin ƙasa.


