Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen jihar Niger ta tabbatar da cewa ɗalibai 50 da aka sace daga makarantar St. Mary’s Catholic da ke Papiri, ƙaramar hukumar Agwara, sun tsere daga hannun masu garkuwa da su.
A wata sanarwa da shugaban CAN na jihar, Bishop Bulus Dauwa Yohanna, ya fitar ranar Lahadi, ya ce yaran sun samu damar kuɓuta ne tsakanin ranar Juma’a da Asabar, kuma sun koma gidajensu cikin natsuwa.
Bishop Yohanna ya bayyana cewa yaran da suka tsere ba su koma makaranta ba kai tsaye, sai daga baya aka gano su bayan an tuntubi iyayensu da ziyartar wasu daga cikinsu.
A cewar sa, daga cikin ɗaliban makarantar firamare 430, guda 377 daliban kwana ne yayin da 53 ke yin jeka ka dawo. Ya ce, baya ga waɗanda suka tsere, akwai sauran ɗalibai 141 da ba a sace su ba.
Ya ƙara da cewa a halin yanzu masu garkuwa da mutane suna riƙe da mutum 253, wanda ya haɗa da:
- 236 dalibai,
- 3 ’ya’yan ma’aikata,
- 14 ɗaliban sakandare,
- 12 ma’aikatan makaranta.


